Isa ga babban shafi
Jamaica

Mutane 73 sun Hallaka a Rikicin Jamaica

Akalla mutane 73 suka hallaka cikin kwanaki hudu da aka kwashe ana kai ruwa rana tsakanin jami’an tsaro da Yan bindigan dake kare mashahurin mai safarar miyagun kwayoyin kasar Jamaica.A cikin adadin akwai fararen hula da Yan bindigan 70, yayin da suaran ukun jami’an tsaro kasar ne.Ministan yada labaran kasar ta Jamaica ya ce babu tabbacin mutumin da ake nema Christopher Dudus Coke ya na cikin kasar.Jami’an tsaro sun ci gaba da shiga gida gida a unguwar da Coke ke rayuwa dake Kingston babban birnin kasar ta Jamaica, da jumman gano shi. Kasar Amurka ta neman Coke ruwa a jallo saboda zargin safarar miyagun kwayoyi. 

Jami'an tsaron Jamaica na dake neman Christoper Coke
Jami'an tsaron Jamaica na dake neman Christoper Coke Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.