Isa ga babban shafi
Madagascar

Sojan Kasar Sunce Babu Ruwansu

Sojan kasar Madagascar sun janye ikirarin da sukayi can baya na dibawa Gwamnatin Andry Rajoelina waadin ya gaggauta kawo karshen rikicin siyasar kasar.Babban Hafsan Sojan kasar, Janar Andre Ndriarijoana wanda ya goyi bayan karbe mulkin kasar da Andry Rajoelina yayi a bara, ya dibawa gwamnatin har karshen watan jiya ne daya gabatar da jadawalin mika mulki ga karbabba  kuma ya shawo kan rigingimun da ake samu da suka haifar da kyamar Gwamnatin daga kasashen waje.Sai dai kuma da yammacin jiya Babban Hafsan Sojan ya fadawa manema labarai cewa ba aikin su ne ba tsara wani abu, domin su 'yan kallo ne.Bayanai na nuna cewa wasu kwamandojin sojan kasar na cike da bakin ciki saboda yadda Shugaban kasar ya gaza warware matsalolin dake addabar kasar.A farkon wannan makon ne Shugaba Andry Rajoelina ya nuna niyyarsa don bullo da sabon tsari, sakamakon gaza samun goyon bayan kaddamar da Gwamnatin hadin kai daga tsoffin Shugabannin kasar da suka hada da Marc Ravalmanana, Didier Ratsiraka da Albert Zafy.  

Andry Rajoelina, le 2 septembre 2009.
Andry Rajoelina, le 2 septembre 2009. rfi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.