Isa ga babban shafi
India-Amurka

India: Amurka ta bukaci daukar matakan gaggawa kan rikicin addini

Hukumar Gwamnatin Amurka dake kula da yancin yin addini a kasashen duniya ta zargi hukumomin India da gazawa wajen daukar matakan da suka dace domin magance rikicin addinin dake gudana a Birnin Delhi, inda ta bukaci daukar matakan gaggawa domin kare Musulmin da basu da rinjaye.

Wani sashin birnin Delhi yayin rikicin addinin da ya barke a India, inda ake musayar jifa da duwatsu tsakanin ambiya addinin Hindu da Musulmi.
Wani sashin birnin Delhi yayin rikicin addinin da ya barke a India, inda ake musayar jifa da duwatsu tsakanin ambiya addinin Hindu da Musulmi. REUTERS/Danish Siddiqui
Talla

Hukumar ta bayyana matukar damuwa kan irin tashin hankalin da ta gani lokacin da shugaba Donald Trump ke ziyarar India.

Shugaban hukumar Tony Perkins, daga bangaren kiristoci masu ra’ayin jiya, yace daya daga cikin hakkin halastacciyar gwamnati shi ne kare lafiyar jama’a da kuma basu tsaro ba tare da la’akari da addininsu ba.

A nasu gefen shugabannin kwamitin Majalisun Amurka kan hulda tsakanin Amurka da India duk sun bayyana damuwa kan abinda yake faruwa, yayin da shugaba Donald Trump yace wannan lamari ne na cikin gidan India, saboda haka ita ta san yadda za ta magance shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.