Isa ga babban shafi
India

Mutane 20 sun halaka a sabon rikicin addinin da ya barke a India

Hukumomin kasar India sun ce mutane 20 yanzu haka aka tabbatar da mutuwar su sakamakon tarzomar da ta barke, wadda ta zama rikicin addini, yayin da 189 suka samu raunuka, kuma kusan 60 daga cikin su harbin bindiga ne.

Wani sashin birnin Delhi da masu tarzoma suka tafka barna yayin sabon rikicin addinin da ya barke a India.
Wani sashin birnin Delhi da masu tarzoma suka tafka barna yayin sabon rikicin addinin da ya barke a India. REUTERS/Danish Siddiqui
Talla

Sunil Kumar dake aiki a asibitin Guru Teg Bahadur yace yanzu haka suna cigaba da kula da wadanda suka samu raunuka, bayan ya tabbatar da mutuwar mutane 20.

Ministan Delhi Arvind Kejriwal ya bukaci gwamnati ta kafa dokar hana fita domin dakile tashin hankalin da kuma baza sojoji akan titunan birnin.

Hargitsin wanda shi ne mafi muni baya bayan nan, ya kai ga kona gidaje da ababan hawa masu tarin yawa.

Tun a ranar lahadi aka fara take-taken bore, don adawa da doka rijistar dan kasa da wasu ke ganin hanya ce tayiwa Musulmin dake kasar kora da hali.

Tsawon Talata ‘yan sanda na ta amfani da karfin tuwo domin kwantar da tarzomar da kuma hana ganin tarukan mutane a wuri guda don gudun cigaba da yaduwar tashin hankalin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.