Isa ga babban shafi
Saudiya

Matan Saudiya na busa sigari da sunan 'yanci

Ana samun karuwar matan da ke busa taba sigari da kuma shisha a bainar jama’a a Saudiya ba tare da fuskantar tsangwama ba.

Mata sun fara shan sigari a bainar jama'a a Saudiya saboda samun 'yanci.
Mata sun fara shan sigari a bainar jama'a a Saudiya saboda samun 'yanci. FRANCE 24
Talla

A yayin zantawa da Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP, daya daga cikin matan Saudiya mai suna Rima ‘yar shekaru 17 da ke aiki a wani kamfani na birnin Riyadh, ta ce, busa sigari a bainar jama’a na cikin ‘yancinta da ta samu a baya-bayan nan.

Rima wadda ta fara zukar sigari shekaru biyu da suka gabata, ta yi watsi da illar da tabar ke yi wa lafiyar bil'adama, amma ta nuna cewa, ba ta son danginta su gano cewa tana shan taba.

Kodayake ta ce, a shirye take ta kare kanta a gaban dangin nata saboda mata na da 'yancin shan sigari kamar takwarorinsu maza.

Masharhanta na danganta hakan da tasirin sauye-sauyen tattalin arziki da zamantakewa ciki har da bai wa matan ‘yanci da Yarima mai jiran gado Muhammed Bin Salman ke aiwatarwa.

A halin yanzu mata na da ‘yancin tuki da kansu, da halartar filayen wasanni da bukukuwan kalankuwa, da kuma damar yin tafiye-tafiye ba tare da muharraminsu ba, abubuwan da a shekarun baya aka haramta musu

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.