Isa ga babban shafi

WHO zata kawar da bayanan karya kan cutar Murar Mashako

Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya tace tana aiki tukuru domin kawar da bayanan karya da ake yadawa ta kafofin sada zumunta kan cutar Murar Mashako ta corona da ta barke a China.

Matakan kariya daga cutar murar Mashako ta Corona
Matakan kariya daga cutar murar Mashako ta Corona REUTERS/Lim Huey Teng
Talla

Shugaban hukumar Tedros Adhanom Gebreyesus ya bayyana haka, yayin da yake gargadi kan yadda wasu mutane ke yada bayanan karya kan cutar.

Wannan na zuwane a dai-dai lokacin da jami’an lafiya a China suka ce adadin mutanen da annobar murar mashako ta corona ta halaka a kasar ya kai kusan 400.

Karuwar adadin na zuwa ne sa’o’i bayan da Philippines ta zama kasa ta farko da ta bada rahoton salwantar rai a dalilin wannan annoba, bayan bazuwar ta zuwa kasashe 24.

Da safiyar wannan litinin ce dai Ma’aikatar lafiyar kasar ta China, ta tabbatar da karuwar adadin wadanda annobar murar ta corona ta halaka daga 304 a ranar lahadi zuwa 361, yayinda kuma adadin wadanda suka kamu da cutar ya karu zuwa dubu 17da 205, bayan da annobar ta harbi wasu karin mutane dubu 2 da 829 a ranar lahadi kadai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.