Isa ga babban shafi
Iraqi

Jami'an tsaron Iraqi sun fatattaki masu zanga-zanga

Jami’an tsaron Iraqi sun fatattaki dubban jama’ar dake zanga-zangar neman tilastawa gwamnatin kasar da Fira Minista Adel Abdul Mahadi ke jagoranta yin murabus, matakin da ya haifar musu da fargabar, za a iya amfani da karfi iko wajen murkushe sauyin da suke nema.

Masu zanga-zangar adawa da gwamnatin Iraqi a Bagadaza.
Masu zanga-zangar adawa da gwamnatin Iraqi a Bagadaza. REUTERS/Thaier al-SudanI
Talla

Rahotanni sun ce an yi arrangama tsakanin masu zanga-zangar da jami’an tsaro a birnin bagadaza, gaf da babban filin taro na Tahrir.

An dai tarwatsa zanga-zangar adawa da gwamnatin ne a Bagadaza inda aka bindige mutane 3, kwana guda, bayan da fitaccen malami Moqtada al Sadr ya yi shelar janye goyon bayan da yake baiwa masu fafutukar sauya gwamnatin, jim kadan bayan jagorantar tasa zanga-zangar ta neman tilastawa sojojin Amurka da kawayensu ficewa daga kasar Iraqi.

A farkon watan Janairu majalisar kasar Iraqi ta kada kuri’ar amincewa da kudurin korar sojojin Amurka, saboda keta mata haddin ‘yanci da Amurkan tayi, ta hanyar kai farmakin sojin da ta kashe babban kwamandan Iran Qasem Soleimani ba tare da neman izinin daukar mataki acikin kasar ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.