Isa ga babban shafi

Adadin mutanen da murar mashako ta hallaka sun kai 17 a China

Annobar cutar murar mashako da ke kamancceniya da SARS wadda ta hallaka mutane 17 a China yanzu haka ta isa Amurka dai dai lokacin da mahukuntan Chinan ke gargadi kan daukar matakan gaggawa don dakile yaduwarta ta hanyar tsaftace gari baya ga gaggauta sanar da jami’an lafiya matukar aka samu rahoton bullarta.

Asibitin da ake kula da masu dauke da cutar murar mashako a yankin Wuhan na China.
Asibitin da ake kula da masu dauke da cutar murar mashako a yankin Wuhan na China. AFP
Talla

Annobar cutar ta murar mashako mai kamanceceniya da SARS wadda yanzu haka ta hallaka mutane 17 a China, ta tayar da hankulan jama’a ne bayan karuwar masu dauke da ita da kuma yadda ta yi saurin fantsama zuwa kasashen ketare, ciki har da Amurka.

Gwamnatin China dai ta sanar da matakan gaggawa don hana cutar yaduwa dai dai lokacin da ake gab da fara bukukuwan sabuwar shekarar yankin.

Cikin matakan ma’aikatar lafiyar China hadda tabbatar da tsaftar tituna da wuraren taruwar jama’a baya ga tabbatar da samuwar wadatacciyar iska musamman a tashoshi da cikin jiragen kasa da na sama dama cikin motocin safa.

Ka zalika karkashin matakan ma’aikatar lafiyar ta China, mahukuntan sun hana taruwar jama’a yayinda aka dakatar da duk wasu taruka musamman a yankin Wuhan da cutar ta tsananta, ciki har da wasannin kwallon kafa da aka janye gudanar da shi a yankin,mai yawan jama’a fiye da miliyan 11 da yanzu haka ake da fiye da mutane 200 da suka kamu da cutar ta murar mashako mai saurin yaduwa.

Tuni dai kasashen duniya ciki har da Birtaniya suka daura damarar hana bazuwar cutar a yankunansu musamman bayan kamuwar mutum guda a Amurka.

Baya ga mutane 440 da suka kamu da cutar ta murarmashako a sassan China, akwai kuma wasu mutane dubu 1 da 394 da yanzu haka ke karkashin kulawar jami’an lafiya don tabbatar da ko sun kamu da cutar mai kamanceceniya da SARS wadda a shekarar 2002 zuwa 2003 ta hallaka mutane 650 a China da Hong Kong.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.