Isa ga babban shafi
Iran-Canada

Iran ta sha alwashin hukunta masu hannu a kakkabo jirgin Ukraine

Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani ya sha alwashin hukunta wadanda ke da hannu a kuskuren harba makami mai linzamin da ya samu jirgin saman Ukraine dauke fasinja 176, inda a bangare guda shugaban ya nemi yafiyar duniya kan abin da ya kira kuskuren da Iran ba za ta iya yafewa kanta ba.

Shugaban Iran Hassan Rouhani.
Shugaban Iran Hassan Rouhani. Official President website/Handout via REUTERS
Talla

Kalaman na Rouhani na zuwa ne da yammacin yau Asabar bayan da sabon bincikensu a daren jiya juma'a ya gano yadda guda cikin makamansu masu linzami 22 da suka harba sansanin Sojin Amurka a Iraqi ya taba jirgin na Ukraine tare da hallaka ilahirin fasinjan da ke cikinsa, ciki har da Iraniya.

Firaministan Canada Justin Trudeau wanda ke da kaso mai yawa na 'yan kasarsa da hadarin ya rutsa da su, ya bukaci Iran ta basu gamsassun bayanai da hujjojin kan yadda ta yi kuskuren kakkabo jirgin Ukraine dauke da fasinja 176 galibi ‘yan Canada a tsakiyar makwan nan.

Trudeau yayin zantawarsa da Shugaban Iran Hassan Rouhani yau Asabar bayan da Iran ta amsa kuskuren kakkabo jirgin, ya bayyana cewa wajibi ne Iran ta dauki alhakin haddasa hadarin jirgin ko da dai ya ce akwai matakai da dama da za su biyo baya.

Tuni dai kwararru na musamman kan binciken hadarin jirgin suka kama hanyar Iran daga Canada inda Iran ta sha alwashin basu cikakken hadin kai wajen ganewa idon dalilan da suka haddasa hadarin.

Kasashen Duniya da dama dai na neman karin gamsassun bayani kan yadda hadarin ya afku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.