Isa ga babban shafi
Oman-Saudiya

Gabas ta tsakiya na makokin Sultan Qaboos na Oman

Kasashen yankin Gabas ta tsakiya da sauran takwarorinsu na ci gaba da alhinin mutuwar Sarkin Oman Sultan Qaboos da ya koma ga mahaliccinsa yau Asabar, Cikin sakon da sarki Salman na Saudiya da yarima mai jiran gado Muhammad bin Salman suka aike, sun bayyana Sultan Qaboos a matsyin jigo ga yankin.

Marigayi sarkin Oman Sultan Qaboos bin Said.
Marigayi sarkin Oman Sultan Qaboos bin Said. Reuters/Fadi Al-Assaad
Talla

Shima Sheikh Khalifa bin Zayed Al-Nahyan na hadaddiyar daular larabawa ya bayyana Sultabn Qaboos a matsayin jajirtacce da ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidimtawa al’ummar Oman yayinda Sarkin Quwait Sabah Al-Ahmad Al-Sabah ya jajantawa al’ummar.

A bangare guda kasashen Masar, Bahrain da Jordan sun bayyana mutuwar Sultan Qaboos a matsayin babban rashi ba kadai ga kasashen larabawa ba, har ma da sauran kasashen duniya.

Sauran kasashen da suka aike da nasu sakon ta’aziyyar akwai India inda Narendra Modi ya wallafa sakon ta'aziyyarsa a shafinsa na twitter yana mai bayyana Sultan Qaboos a matsayin kamilin shugaba kuma jagoran ga kasashen larabawa, yayinda Firaminista Boris Johnson na Birtaniya ya jajantawa al'ummar kasar.

Shima da ya ke aikewa da nasa sakon ta'aziyyar tsohon shugaban Amurka George W Bush bayyana Sarkin ya yi a matsayin wanda ke hidimtawa al'ummarsa kuma tsayayye.

Tuni dai masarautar ta Oman ta sanar da sunan Sultan Haitham bin Tariq Al-Said a matsayin wanda zai gaji Qaboos, inda cikin sakon karbar rantsuwar kama aiki, Sultan Haitham ya sha alwashin dorawa kan abubuwan da Sultan Qaboos ya faro.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.