Isa ga babban shafi
Amurka-Iran

Harin jiragen Amurka ya hallaka babban kwamandan Sojin Iran

Harin jiragen Amurka marasa matuka a safiyar yau Juma'a ya hallaka babban kwamandan Sojin Iran a Iraqi Qasem Soleiman, matakin da ya kara tsamin alaka tsakanin kasashen biyu, yayinda a bangare guda kuma dubun dubatar Iraniyawa ke gudanar da gangamin nuna adawa da ta’addanci Amurkan.

Shugaban kasar Iran Hassan Rohani tare da Marigayi Qassem Soleimani, babban kwamandan Sojin kasar.
Shugaban kasar Iran Hassan Rohani tare da Marigayi Qassem Soleimani, babban kwamandan Sojin kasar. AFP/Présidence iranienne
Talla

Dubban Iraniyawan da ke nuna alhininsu da kisan Qasem Soleiman sun yi dafifi a manyan titunan birnin Tehran bayan sakkowa daga sallar Juma’a, jim kadan bayan da ma'aikatar tsaron Iran ta sha alwashin daukar mataki kan kisan.

Zanga-zangar Iraniyawan na zuwa dai dai lokacin da a can Iraqi kuma wajen da harin ya faru Amurka ta yi umarnin gaggauta kwashe al’ummarta da ke sassan kasar.

Baya ga Babban Hafson Sojin na Iran da harin jirgin Amurkan ya hallaka har da Abu Mahdi al-Muhamdis shugaban mayakan sa kai duk dai a yau Juma’ar.

Ma’aikatar tsaron Amurka ta bayyana cewa jiragen na ta marasa matuka sun farmaki motocin Soji 2 a filin jirgin saman birnin Baghdad da ya yi sanadin mutuwar Qasim Soleiman da Abu Mahdi.

Sanarwar ma’aikatar ta nuna cewa yanzu dakarunta na musamman 750 sun isa Baghdad wadanda za su baiwa Amurkawa kariya a Ofishin jakadancin Amurkan da ke birnin na Baghdad.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.