Isa ga babban shafi
Indiya

Ba don muzguna wa Musulmi muka yi dokar rajistar dan kasa a Indiya ba - Modi

Firaministan India Narendra Modi ya yi jawabin kwantar wa da Musulmai hankula, yayin da mummunar zanga – zanga ke ci gaba da kamari a kasar kan sabuwar dokar zama dan kasa, lamarin da ya jefa gwamnatinsa cikin matsin lamba.

Firaministan India Narendra Modi
Firaministan India Narendra Modi Nicholas Kamm / AFP
Talla

Da yake jawabi ga magoya bayansa a birnin New Delhi, Modi ya bukaci Musulmai da kada su tayar da hankulansu idan har su ‘yan asalin Indiya ne, yana mai cewa dokar ba ta shafi wadanda aka Haifa a kasar ba.

Da yake zargin babbar jam’iyyar adawa da yin na’am da tarzomar da ta barke sakamakon zanga zangar, ta wajen rashin yin tir da lamarin, Modi ya ce abokan hamayya na yada jita – jitar karya cewa gwamnatinsa za ta tura daukacin Musulmin kasar sansanonin ihun ka banza.

Bugu da kari, Modi ya musanta cewa akwai wani shirin yin rajistar gama – gari, wacce akasarin Musulman Indiya ke fargabar cewa don muzguna musu za a yi.

A cikin wannan shekarar, irin wannan rajistar ta sa mutane kusan miliyan biyu cikin halin kaka ni ka yi a jihar Assam, inda suka kasa nuna cewa kakaninsu na jihar kafin shekarar 1971, abin da ya sa yanzu suke cikin hatsari rasa inda zasu kira jiharsu.

Akalla mutane 25 ne suka mutu a zanga – zangar da aka kwashe makkonni biyu ana yi, kuma ko a a wannan Lahadi, an samu karin zanga – zanga a wasu yankuna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.