Isa ga babban shafi

Bangarorin siyasar Lebanon na tattaunawa don kafa sabuwar gwamnati

Shugaban kasar Lebanon Michel Aoun na tattaunawa da bangarorin siyasar kasar, yau Alhamis domin zaben wanda zai maye gurbin Franminista Sa’ad Hariri da zanga-zanga ta tilastawa yin murabus makonnin baya.

Masu zanga-zangar adawa da gwamnati rike da tutoti a kasar Lebanon
Masu zanga-zangar adawa da gwamnati rike da tutoti a kasar Lebanon REUTERS/Mohamed Azakir
Talla

Shugaba Michel Aoun ya kaddamar da zaman tattaunawar da aka jinkirta yunkurinsa har sau biyu domin zabin sabon Firayim Ministan.

Sa’ad Hariri, wanda zanga-zangar adawa da gwamnati ta tilastawa Murabus ranar 29 ga watan Oktoba, na daga cikin wadanda shugaban ke tattaunawa da su.

Har yanzu wasu na ganin Hariri mai shekaru 49 a duniya mabiyi akidar sunni, a matsayin wanda yafi cancanta ya jagoranci sabuwar gwamnatin Lebanon, ganin kwarewarsa da sanin siyasar duniya.

Sai dai kash, ko a daren Laraba ya jadda da matsayin kauracewa sabuwar gwamnatin da ake shirin kafawa, kazalika yaki bayyana ko zabin dan takarar da zai gaje shi.

Yanzu haka hankula sun karkata kan Hassan Diab, malamin Jami'ar Amurka dake Beirut kuma tsohon ministar ilimin kasar, wanda kafofin yada labaran Lebanon suka bayyana amatsayin magajin Hariri.

Kuma shine mutumin da Kungiyar mazahaba akidar shi’a ta Hezbollah da kawancen jam’iyyar siyasarta ke da rinjaye a majalisar dokokin kasar ta zaba, sai dai kuma bangaren takwarorinsu na Sunni na adawa da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.