Isa ga babban shafi
Iraq

An sanya dokar ta - baci a Iraki bayan mutuwar mutane 13

Hukumomi a Iraki sun bayyana sanya dokar takaita walwala a Nasiriyah dake kudancin kasa a Alhamis, bayan harbe mutane 13 har lahira a diran mikiyar da jami’an tsaro suka yi wa masu zanga –zangar kin jinin gwamnati.

Masu zanga - zanga a Iraki dauke da wani mutumin da barkonon tsohuwa ya wa illa.
Masu zanga - zanga a Iraki dauke da wani mutumin da barkonon tsohuwa ya wa illa. REUTERS/Thaier al-Sudani
Talla

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ruwaito cewa an girke jami’an tsaro ko ina a gefen birnin, inda suke binciken duk wani abin hawa dake kokarin shiga birnin.

Wannan ya biyo bayan sanya dokar ta - baci ne a birnin mai tsarki na Najaf, bayan damasu zanga – zanga suka banka wa ofishin jakadancin Irandake yankin wuta cikin dare.

Firaministan Iraki dayarasa tagomashin sa, Adel Abdel Mahdi ya aike damaanyan kwamandojin soji da dama zuwa lardunan dazanga – zangar ta yi kamari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.