Iran: Masu bore sun kashe jami'an tsaro
Masu bore a Iran sun kashe jami’an tsaron kasar 3 ta hanyar daba musu wuka a yammacin birnin Teheren.
Wallafawa ranar:
Zuwa yanzu mutane 5 aka tabbatar da mutuwarsu yayin zanga-zangar da ta barke a wasu biranen kasar ta Iran a ranar Juma’a, bayan da gwamnati ta sanar da karin farashin man fetur da kashi 50 cikin 100, da.
Shugaban Iran Hassan Rouhani ya ce karin farashin man fetur din zai taimakawa kasar samun karin kudaden shigar da adadinsu ya kai dala biliyan 2 da miliyan 55 a shekara, kwatankwacin kudin kasar Rial triliyan 300.
Matakin kara farashin man a Iran ya zo ne kwanaki kalilan bayan sanar da gano arzikin gangar danyen mai akalla biliyan 53 kwance a wani fili dake kudancin kasar.
Yazu haka dai Iran na kan fama da takunkuman karya tattalin arzikin da shugaba Donald Trump ya kakaba mata, bayan janye Amurka daga yarjejeniyar nukiliyar da Iran din ta cimma da manyan kasashen Turai a shekarar 2015.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu