Isa ga babban shafi

Dakarun China na aikin tsaftace Hong Kong

Sojoji China sun shiga gari daga barikinsu dake Hong Kong, domin taimakon tsabtace birnin daga abubuwan da masu zanga-znagar tabbatar da demokradiyya sukayi amfani da su, tsawon mako guda.

Dakarun China kenan a yankin Hong Kong suna taimakon kwashe sharar da masu zanga-zanga suka zubar. 16 ga watan Nuwamba 2019
Dakarun China kenan a yankin Hong Kong suna taimakon kwashe sharar da masu zanga-zanga suka zubar. 16 ga watan Nuwamba 2019 AFP / HKFP
Talla

Sai dai gwamnatin yankin Hong-Kong mai kwarya-kwaryan yanci, ta ce, bata bukaci wannan taimako ba daga dakarun na kasar China.

A baya dai kafar yada labaran gwamnatin China ta ruwaito cewa, mai yiwuwa China ta tura dakarunta don dakile rikicin da yaki ci yaki cinyewa a yankin tsawon watanni shida.

A baya-bayan nan wani jami’in ‘yan sandan Hong Kong ya harbe daya daga cikin masu zanga-zangar neman tabbatar da dimokradiya a yankin, yayin da a gefe guda aka cinna wa mutum guda wuta sakamakon husumar da ta barke tsakaninsa da wani.

Masu zanga-zangar sun mayar da martani kan harbin da aka yi wa dan uwansu a sanfin safiyar wannan Litinin, inda suka tayar da hatsaniya a tashoshin jiragen kasa tare da datse tituna baya ga farfasa shaguna.

A daidai lokacin da aka yi harbin ne wani mahari rufe da fuskarsa ya cinna wa wani mutum wuta bayan ya tiltila masa wani abu mai kama da man fetur a jiki, yayin da aka nadi hoton bidiyon wannan al’amari mai tayar da hankali kuma aka watsa kai tsaye ta kafar Facebook.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.