Isa ga babban shafi

Pakistan ta gabatar da sabon rigakafin cutar Typhoid

Pakistan ta zama kasa ta farko a Duniya da ta gabatar da sabon rigakafin maganin kamuwa da cutar ‘typhoid’, sakamakon barkewar nau’in cutar dake bijirewa magunguna a kasar.

Gojin kwayoyin cutar Typhoid
Gojin kwayoyin cutar Typhoid Getty/R Parulan Jr.
Talla

Za’ayi makwanni biyu ana bada rigakafin maganin da Hukumar Lafiyar ta Majalisar Dinkin Duniya ta amince da shi a kudancin Yankin Sindh da aka samu mutane sama da 10,000 da suka kamu da cutar a shekarar 2017.

Azra Pechuho, ministar lafiyar Yankin tace akalla mutane miliyan 10 ake saran su karbi rigakafin a cikin makwanni biyu tsakanin masu watanni 9 zuwa shekaru 15.

A shekarar 2017 kashi 63 na masu fama da cutar sun fito daga yankin Sindh ne, kuma kashi 70 daga cikin su sun mutu su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.