Isa ga babban shafi
iran

Iran ta gano fili mai dauke da gangar danyen mai biliyan 53

A Lahadin nan shugaban Iran Hassan Rouhani ya sanar da cewa kasar ta gano wani fili dake kunshe da gangar danyen mai har biliyan 53.

Shugaban Iran Hassan Rouhani
Shugaban Iran Hassan Rouhani © REUTERS/Brendan Mcdermid
Talla

Filin ya kai muraba’in kilomita 2,400, kuma yana garin Khuzestan ne a kudu maso yammacin kasar, kamar yadda Rouhani ya fada a wata ganawa ta talabijin.

Rouhani ya ce rijiyar man mai zurfin mita 80 ya kai nisan kilomita 200 daga iyakar Khuzestan da Iraqi zuwa birnin Omidiyeh.

Iran na cikin kasashen da suka kafa kungiyar kasashe masu arzikin danyen mai, kuma ita ce kasa ta hudu a duniya da ke da dimbin arzikin mai, amma tana samun matsala wajen sayar da man ta tun da shugaban Amurka Donald Trump ya janye daga yarjejeniyar nukilyar 2015, ya kuma kakaba mata takunkumai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.