Isa ga babban shafi
India

Hazo ya turnuke birnin Delhi na India

Miliyoyin mazauna birnin New Delhi na India sun tashi da matsalar hazo mai hana mutane hangen nesa da kuma sanya radadi a ido, matsalar da ta tilasta rufe makarantu da hana motoci zirga-zirga da kuma dakatar da ayyukan gine-gine.

Yadda hazo ya gurbata birnin New Delhi na India
Yadda hazo ya gurbata birnin New Delhi na India REUTERS/Anushree Fadnavis
Talla

An dai saba ganin irin wannan hazon a kowacce shekara sakamakon hayakin motoci da sinadaren da masana’antu ke fitarwa da kuma kona amfanin gonaki.

Ministan Birnin Delhi Arvind Kejriwal ya bukaci daukar matakai domin kawo karshen gurbata muhallin da ya ke haifar da matsalar wadda ke hana matasa da tsoffi numfashi.

Jami’an kiwon lafiya sun bukaci jama’a da su ci gaba da zama a gidajensu domin kauce wa kamuwa da matsalar numfashi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.