Isa ga babban shafi
Lebanon

Zanga-zangar Lebanon na ci gaba da tsananta

Dai dai lokacin da zanga-zangar Lebanon ke ci gaba da tsananta Firaministan kasar Sa’ad Hariri ya bai wa mukarraban gwamnatin hadakarsa wa’adin sa’o’I 72 don amincewa da sabon kudirin yiwa tattalin arzikin kasar gyaran fuska wanda ya kunshi kara harajin da ya fusata al’umma.

Dubunnan al'ummar Lebanon da ke kalubalantar halin da tattalin arzikin kasar ke ciki.
Dubunnan al'ummar Lebanon da ke kalubalantar halin da tattalin arzikin kasar ke ciki. REUTERS/Mohamed Azakir
Talla

Matakin Hariri wanda ke zuwa duk da tsanantar zanga-zangar kasar da ta firgita hatta makotan kasashen larabawa, Firaministan ya zargi jami’an gwamnatin hadakarsa da hannu wajen hana gudanar da gyaran fuskar wanda zai daidaita tattalin arzikin kasar.

Shugaba Hariri ya zargi bangaren adawa da kuma kungiyar Hezbollah mai samun goyon bayan Iran a matsayin wadanda ke yiwa sabbin tsare tsarensa zagon kasa.

Tuni dai Kasashen Larabawa ciki har da jagora a yankin gabas ta tsakiyan Saudi Arabia su ka gargadi al’ummominsu da su kauracewa yankunan da zanga-zanga ke ci gaba da gudana a Lebanon.

Cikin sanarwar da Ofishin jakadancinSaudiyan a Lebanon ya fitar ya bukaci ‘yan Saudiya da ke shirin ziyartar kasar ta Lebanon su dakatar da tafiye-tafiyensu yayinda ya bukaci wadanda ke cikin kasar su kauracewa yankunan da zanga-zangar ke faruwa.

Sauran kasashen da suka fitar da makamanciyar sanarwar sun hada da Masar da hadaddiyar daular larabawa da kuma Kuwait.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.