Isa ga babban shafi
Afghanistan

Fararen hula dubu 1 da 200 sun mutu cikin watanni 3 a Afghanistan

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana matukar kaduwar ta da yawan adadin fararen hular da suka mutu a kasar Afghanistan tsakanin watan Yuli zuwa Satumbar bana, inda take cewa wannan lamari ba abinda za’a amince da shi bane.

Wani harin Taliban a Afghanistan
Wani harin Taliban a Afghanistan NOOR MOHAMMAD / AFP
Talla

Tadamichi Yamamto, jami’in Majalisar Dinkin Duniya da ke Kabul ya ce tsakanin ranar 1 ga watan Yuli zuwa 30 ga watan Satumba, mutane dubu 1 da 174 aka kashe, yayin da aka jikkata dubu 3 da139, wanda ya nuna karuwar kashi 42.

Jami’in ya ce adadin da aka samu na watan Yuli ya zarce na kowanne wata.

Tun bayan tabarbarewar tattaunawar Taliban da Amurka ne, kungiyar ta ci gaba da tsananta hare-hare inda galibin wadanda hare-haren na ta kan shafa fararen hula, ciki har da masu kada kuri'a a zaben kasar da ya gudana.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.