Isa ga babban shafi
Hong Kong

Zanga-zangar Hong Kong ta gurgunta sufuri da kasuwanci

Mafi akasarin tashoshin jiragen kasa a yankin Hong Kong na ci gaba da kasancewa a rufe, bisa fargabar abinda zai biyo bayan zanga-zangar da dubban masu neman kafa tsarin mulkin dimokaradiya suka sha alwashin ci gaba da yi a yau Lahadi.

Daya daga cikin manyan tashoshin jiragen kasa a Tseung Kwan O, dake yankin Hong Kong, bayan da masu zanga-zanga suka lalata kayayyaki a tashar. % gawatan Oktoba, 2019.
Daya daga cikin manyan tashoshin jiragen kasa a Tseung Kwan O, dake yankin Hong Kong, bayan da masu zanga-zanga suka lalata kayayyaki a tashar. % gawatan Oktoba, 2019. YAN ZHAO / AFP
Talla

Zanga-zangar ta yau na zuwa ne a daidai lokacin da su kuma ‘yan majalisar yankin na Hong Kong daga bangaren ‘yan adawa suka garzaya kotu, don kalubalantar dokar haramtawa masu zanga-zanga rufe fuskokinsu da ta soma aiki a ranar asabar.

An dai shafe watanni 4 wannan zanga-zanga tana gudana a Hong Kong wadda aka soma kan adawa da kudirin dokar mika masu laifi daga yankin zuwa China, daga bisani kuma ta rikide zuwa ta neman fita daga karkashn China, da komawa kan tsarin dimokaradiya.

Ranar Juma’a shugabar yankin na Hong Kong Carrie Lam, ta sanar da haramtawa masu zanga-zangar rufe fuskokinsu, a karkashin wata dokar ta baci da ta soma aiki a yau, da aka kwashe sama da shekaru 50 ba a yi amfani da ita ba a yankin.

Sai dai a maimakon dokar ta bacin ta sassauta tashin hankalin da yankin ke ciki, sai ta kara fusata masu zanga-zangar, lamarin da ya haddasa arrangama maras kyau tsakaninsu da jami’an tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.