Rikicin Iraqi: Tilas kowa ya shiga taitayinsa - MDD
Babbar jami’ar Majalisar Dinkin Duniya a Iraqi ta yi tir da rikicin da ya tashi a Iraq biyo bayan zanga – zangar kwanaki biyar da ya yi sanadin mutuwar kusan mutane 100 tare da jikkata dubbai a kasar,tana mai cewa dole a daina salawanta rayuka.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
"kwanaki biyar na kisa da jikkata mutane bai yi ba, dole a daina," a cewar Jeanine Hennis-Plasschaert, wakiliyar babban sakaren majalisar Dinkin Duniya a Iraqi, a wani sakon tweeter da ta wallafa.
Hukumar kare hakkin dan adam ta majalisar dokokin Iraqi ta ce mutane 99 ne suka mutu, kana dubu 4 suka jikkata tun da aka fara zanga – zangar adawa da rashin ayyukan yi da rashawa a kasar.
Jami’ar Majalisar Dinkin Duniyar ta ce ta hasala da kashe – kashen da ya auku a kasar.
"Ina kira ga dukkan bangarorin da su dakata su yi karatun’ta natsu’. Ya kamata a hukunta wadanda suka haddasa wannan tarzoma. Kamata ya yi hadin kai ya samu gindin zama a Iraqi, " In ji Jeanine.
Zanga – zangar da aka fara don nuna rashin amincewa da yadda rashin aikin yi da rashawa suka yi katutu a kasar ta rikide zuwa wani gangami na neman kawo karshen rashawa tsakanin jami’en gwamnati da ma sauyin gwamnati.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu