Isa ga babban shafi

Adadin wadanda suka mutu a zanga-zangar Iraqi ya zarta 50

Zanga-zangar adawa da gwamnati dake gudana a Iraqi na ci gaba da munana, inda a halin yanzu adadin wadanda suka rasa rayukansu cikin kwanaki hudu ya kai akalla mutane 60.

Wani sashin birnin Bagadaza yayin zanga-zangar adawa da gwamnati.
Wani sashin birnin Bagadaza yayin zanga-zangar adawa da gwamnati. REUTERS/Thaier al-Sudani
Talla

Sai dai cikin rahoton da ta fitar hukumar sa ido kan kare hakkin dan adam a kasar ta Iraqi, ba ta bayyana adadin fararen hula da kuma jami’an tsaron da suka halaka a kazamin boren ba.

Kawo yanzu dai sama da mutane dubu 1 da 600 suka jikkata yayin zanga-zangar da ta rikide zuwa tashin hankali, abinda ya haifar da fargabar cewa adadin wadanda suka rasa rayukansu zai iya karuwa.

Masu zanga-zangar dai sun bijirewa dokar hana zirga-zirga, hayaki mai sa hawaye da ma harbi da alburusai masu rai, inda suka ci gaba da yin tattakin nuna adawa da gwamnatin Fira Minista Adel Abdel Mahdi, kan gazawa wajen magance matsalolin cin hanci da rashawa, rashin ayyukanyi da kuma ababen more rayuwa.

Sai dai Fira ministan kasar ta Iraqi Adel Abdel Mahdi ya bukaci al’ummar Iraqi da su kara hakuri don bai wa gwamnati damar gabatar da wani sabon kudirin gyara da zai magance matsalar aikin yi a kasar.

Wannan dai shi ne bore mafi muni da gwamnatin Fira minista Adel Abdel Mahdi ya gani tun bayan hawansa mulki a shekarar 2018.

A ranar talata zanga-zangar kin jinin gwamnatin ta barke a birnin Bagadaza, inda cikin kwanaki uku ta bazu zuwa biranen kasar akalla 5, ciki har da Babylon, Basra, da Najaf.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.