Isa ga babban shafi
Taliban

Adadin mutanen da suka halaka a hare-haren Kabul ya karu

Adadin mutanen da suka hallaka a jerin hare-haren kunar bakin wake biyu a Kabul babban birnin Afghanistan ya karu daga 24 zuwa 48.

Filin gangamin siyasar da dan kunar bakin wake ya halaka mutane da dama a Afghanistan.
Filin gangamin siyasar da dan kunar bakin wake ya halaka mutane da dama a Afghanistan. AFP/ABDUL SHAHMIM TANHA
Talla

An dai kai hare-haren ne a gaf da wajen gangamin taron yakin neman zabe, wanda shugaban kasar ta Afghanistan Ashraf Ghani ke halarta, yayinda aka kai hari na biyu a cikin birnin Kabul.

A hari na farkon, wani ne a kan babur ya tayar da bam din da ke makale a jikinsa a wani shingen binciken ababen hawa da ke kan hanyar isa ga inda shugaba Ashraf Ghani ke jawabi ga magoya bayansa a tsakiyar lardin Parwan, arewa da babban birnin kasar, nan ne mutane 26 suka mutu, 42 suka jikkata.

Sa’a daya bayan harin, wani bam din ya tashi a Kabul, kusa da ofishin jakadancin Amurka, wanda tun da farko hukumomi ba su bayyana adadin wadanda abin ya rutsa da su ba, amma daga baya suka ce mutane 22 sun kwanta dama, yayin da 38 suka jikkata.

Wadannan hare-hare dai na zuwa ne bayan shugaban Amurka Donald Trump ya dakile tattaunawar da ke gudana tsakanin Amurka da Taliban a farkon wannan wata.

A wata sanarwa daga Taliban kan daukar alhakin harin, mai magana da yawun mayakan Zabihullah Mujahid ya ce sun kai hari wajen gangamin siyasar shugaba Ghani da gangan ne da zummar tarwatsa zaben 28 ga watan Satumba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.