Isa ga babban shafi
Pakistan-India

Pakistan na zargin India da kisan kare dangi a Jummu da Kashmir

Kasar Pakistan ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamar da binciken kwa-kwaf a yankin Kashmir da Jummu mai rinjayen Musulmi bayan kwace kwarya-kwaryar ‘yancin da India ta yi wa yankin a watan jiya.

Firaministan Pakistan Imran Khan
Firaministan Pakistan Imran Khan REUTERS/Stringer
Talla

Ministan harkokin wajen Pakistan Shah Mehmood Qureshi yayin jawabinsa gaban hukumar kare hakkin dan adama ta Majalisar Dinkin Duniya a birnin Geneva, ya ce yanzu haka India na aiwatar da kisan kare dangi a wani yunkuri na shafe al'ummar yankunan biyu masu rinjayen musulmi wato Kashmir da Jummu.

A cewar Shah Mehmood tun daga ranar 5 ga watan Agusta zuwa yanzu India ta katse layukan sadarwa da na Intanet a jihohin Jummu da Kashmir yayinda ta kaddamar da wani shirin kamen babu gaira babu dalili.

Ministan ya bayyana cewa a yanzu haka ba komai ke faruwa a yankunan biyu na Jummu da Kashmir ba, face kisan kare dangi baya ga muzantawa da cin zarafi wanda sojin India ke aikatawa.

Akwai dai rahotanni da ke nuna cewa yanzu haka India ta kame mutane dubu 6 daga yankunan biyu inda ta jefa su a gidajen yari bayan da suka kalubalanci matakin kwace musu kwarya-kwaryan 'yancin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.