Isa ga babban shafi

Amurka za ta janye dakarunta daga Afghanistan cikin kwana 135

Jakadan Amurka a tattaunawarta da Taliban Zalmay Khalilzad ya ce Amurka a shirye take ta janye ilahirin dakarunta daga Afghanistan matukar aka samu cimma yarjejeniyar a tattaunawar bangarorin biyu da ke ci gaba da gudana can a Qatar.

Shugaba Ashraf Ghani yayin tattaunawarsa da Zalmay Khalilzad a Kabul
Shugaba Ashraf Ghani yayin tattaunawarsa da Zalmay Khalilzad a Kabul © Reuters
Talla

A wata tattaunawarsa da Sashen labarai na Tolo News Zalmay Khalilzad ya ce idan har aka kammala kulla yarjejeniya bisa daidaito kan bukatun kowanne bangare, Amurkan za ta janye dakarunta da ke sansanoni 5 a cikin kasar ta Afghanistan a kwanaki 135.

Tuni dai kamfanin labarai na Reuters ya ruwaito cewa, shugaba Ghani ya yi maraba da matakin tare da shan alwashin gabatar da jawabi game da kalaman na Khalilzad.

Sai dai fitar kalaman na Khalilzad a yammacin yau Litinin ke da wuya aka fara jiyo karar musayar bindigu baya ga wata fashewa a wajen birnin Kabul, ko da dai kawo yanzu babu wata masaniya game da dalilin faruwar lamarain.

Wasu hotunan faruwar lamarin a shafukan sada zumunta sun nuna yadda turkukun hayaki ke tashi a wajen birnin sai dai babu bayani kan abin da ya faru ko kuma wadanda ke da hannu a faruwarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.