Gungu-gungu na masu zanga-zangar sun kafa shingaye, tare da kunna wuta kan tituna, gami da jifan ‘yan sanda da kwalabe, yayinda su kuma jami’an tsaron suka maida raddi ta hanyar feshin wuta da harba hayaki mai sa hawaye.
Kudurin dokar mika masu lafi daga yankin na Hong Kong zuwa China ne dai ya soma haddasa gagarumar zanga-zangar, wadda a yanzu ta rikide zuwa ta neman komawar yankin kan tsarin Dimokaradiyya irin na Turai, da samun karin yanzi daga China.
A ranar Juma'a Kungiyar Tarayar Turai ta bayyana rashin amincewa da kamen da hukumomin Hong Kong ke yiwa masu rajin kare dimokradiya, yayinda mahukuntan China suka jaddada cewa sam babu zancen lallashin masu bore da ake yi.
Uwargida Federica Mogherini, mai magana da yawun kungiyar kasashen na Turai ta bukaci ganin mahuntan Hong Kong ta mutunta ‘yancin fadin albarkacin baki, da ‘yancin gudanar da taro.