Saurare Saukewa Podcast
 • 06h00 - 06h17 GMT
  Labarai 16/12 06h00 GMT
 • Labarai 06h00 - 06h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 15/12 06h00 GMT
 • Shirye-shirye 06h06 - 06h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 15/12 06h06 GMT
 • 06h17 - 06h27 GMT
  Shirye-shirye 16/12 06h17 GMT
 • 07h00 - 07h17 GMT
  Labarai 16/12 07h00 GMT
 • Labarai 07h00 - 07h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 15/12 07h00 GMT
 • Shirye-shirye 07h06 - 07h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 15/12 07h06 GMT
 • 07h17 - 07h27 GMT
  Shirye-shirye 16/12 07h17 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h30 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 13/12 16h00 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 15/12 16h00 GMT
 • Shirye-shirye 16h06 - 16h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 15/12 16h06 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 15/12 16h30 GMT
 • Labaran Duniya 16h30 - 16h40 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 13/12 16h30 GMT
 • Shirye-shirye 16h36 - 16h56 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 15/12 16h36 GMT
 • Ra'ayoyin Masu Saurare 16h40 - 16h55 GMT Litinin-Jumma`a
  Jin Ra'ayoyin Masu Saurare 13/12 16h40 GMT
 • Labarai 20h00 - 20h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 15/12 20h00 GMT
 • 20h00 - 20h17 GMT
  Labarai 13/12 20h00 GMT
 • Shirye-shirye 20h06 - 20h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 15/12 20h06 GMT
 • 20h17 - 20h27 GMT
  Shirye-shirye 13/12 20h17 GMT
Domin more wa abubuwan da ke ciki, dole ne a tabbatar da cewa an sanya Flash Domin shiga sai an hada cookies a cikin shafin bincike
Asiya

Sojoji dubu 43 na fafutukar kashe gobarar dajin Amazon

media Wani sashin Amazon da mahaukaciyar gobarar daji ta kone. REUTERS/Bruno Kelly

Sojojin Brazil sama da dubu 43 da taimakon jiragen sama ke ci gaba da kokarin kashe mahaukaciyar gobarar da ke kone dajin Amazon, mafi girma a duniya.

Yanayin na zuwa ne a dai dai lokacin da masana a Brazil suka bada tabbacin sake tashin wutar a Karin wasu sassan na dajin Amazon, da adadinsu ya kai dubu 1 da 130 a tsakanin Juma’a zuwa jiya asabar.

Zalika wata kididdiga da masanan suka fita ya nuna cewa a shekarar da muke ciki kadai an samu tashin gobarar daji a Brazil sau dubu 79 da 513, yanayi mafi muni tun bayan shekarar 2013.

Binciken masanan ya kuma ce mafi akasarin gobarar dajin na aukuwa ne a dajin na Amazon, da masana kimiyya ke yiwa lakabi da huhun duniya, la’akari da cewa yana taka rawar fitar da kashi 1 bisa 5 na iskar Oxygen dadan adam ke shaka.

Tuni dai shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce kasashen G7 da yake karbar bakuncin taronsu, za su tallafawa kasashen da Gobarar Dajin Amazon ta shafa, cikin gaggawa.

Gobarar dake barazana ga dajin na Amazon dai ta shiga cikin muhimman batutuwan da taron kasashen 7 masu karfin tattalin arziki ke tattaunawa a kai.

Kashi 60 cikin 100 na dajin Amazon din na cikin kasar Brazil ne, sai dai dajin da akai ittifakin shi ne mafi girma a duniya ya ratsa ta cikin Karin kasashe 8 daga cikinsu kuma akwai, Bolivia, Colombia, Peru, Vanezuela da kuma Ecuador.

A game da wannan maudu'i
Sharhi
 
Yi hakuri lokacin ci gaba da kasancewa da mu ya kure