Isa ga babban shafi

India ta zargi Pakistan da haddasa ayyukan ta'addanci a Kashmir

Firaministan India Narendra Modi ya ce matakin kwace kwarya-kwaryar ‘yancin cin gashin kan yankin Kashmir mai rinjayen musulmi na da nufin ceto yankin daga barazanar Pakistan ta fadada ayyukan ta’addanci da kuma cusa akidar wariya tsakanin al’ummar yankin.

Firaministan India Narendra Modi
Firaministan India Narendra Modi REUTERS/Amit Dave
Talla

Cikin jawaban da ya gabatar, wanda shi ne karon farko tun bayan daukar matakin kwace kwarya-kwaryan ‘yancin na Kashmir, Firaministan India, Narendra Modi ya ce matakin na da nufin ceto yankin ba wai muzanta masa ba.

A cewar Modi wanda ke jawabi dai dai lokacin da India ta girke tarin jami’an tsaro a yankin na Kashmir, yana da yakinin sabon matakin zai taimaka matuka wajen ceto al’ummar Kashmir da Jummu daga barazanar tsaron da su ke fuskanta daga Pakistan.

Firaministan na India ya yi zargin cewa Pakistan na amfani da yankin na Kashmir wajen kaddamar da ayyukan ta’addanci a India wanda kuma ya ce bayan wannan matakin, ya yi imanin cewa Kashmir za ta mike tsaye wajen fatattakar ayyukan ta’addanci.

Cikin jawaba na Narendra Modi dake zuwa dai dai lokacin da Firaministan Pakistan Imran Khan ke cewa baya da shirin amfani da karfin Soji a yankin na Kashmir bayan matakin India na girke tarin jami’an tsaro, Modi ya bayyana matakin da babbar nasara kan abokiyar gabarsu Pakistan.

A cewar Modi Pakistan na gurbata tunanin al’ummar yankunan na Kashmir da Jummu don su juya baya ga India, matakin da ke matsayin babbar barazanar tsaro ga New Delhi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.