Isa ga babban shafi

Za mu iya tattaunawa da Amurka don zaman lafiyar duniya- Rouhani

Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani ya ce kasar za ta iya tattauanwa da Amurka matukar ta janye takunkuman da ta kakaba mata, matakin da ke zuwa dai dai lokacin da bayanai ke nuna babban jami’in Diflomasiyyar shugaban ya yi watsi da gayyatar Donald Trump a watan jiya.

Shugaban Iran Hassan Rouhani
Shugaban Iran Hassan Rouhani REUTERS/Abdullah Dhiaa Al-Deen
Talla

Rouhani wanda ke jawabi gaban manema labarai a ma’aikatar harkokin wajen kasar bayan ganawarsa da babban jami’in Diflomisyyar kasar kuma ministan harkokin wajenta Mohammed Javad Zarif, ya ce sulhu da Iran shi ne mafarin kowanne zaman lafiya a duniya.

Cikin kalaman na sa, Rouhani ya bayyana cewa yaki da Iran tamkar taso da yaki ne a sassa daban-daban na duniya, kamar yadda zaman lafiyar Iran zai zaunar da duniya lafiya.

Haka zalika shugaban an Iran Hassan Rouhani ya bayyana cewa ci gaba da mutunta yarjejeniyar 2015 da suka kulla da manyan kasashen duniya ita ce hanya daya da wanzar da zaman lafiya a duniya.

Sai dai Raouhani ya ce Iran za ta bude kofar tattaunawar ne tsakaninta da Amurka idan har Amurkan ta bukaci haka.

A cewar Rouhani ya ragewa Amurka a yanzu haka ta janye takunkuman tare da neman sulhu da Iran ko kuma aci gaba da halin da ake ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.