Isa ga babban shafi
Gabas ta tsakiya

Bahrain na karbar taron kwamandojin Sojin ruwan yankin Gulf

Kasar Bahrain na daukar nauyin taron manyan kwamandojin sojin ruwan kasashen yankin Gulf, a daidai lokacin da ake zaman tankiya da Iran sakamakon kama jiragen dakon mai a mashigin ruwan Hormuz.

Taron dai na da nufin samar da tsaro a mashigin ruwan Hormuz bayan hare-haren Iran kan jiragen ruwan Birtaniya
Taron dai na da nufin samar da tsaro a mashigin ruwan Hormuz bayan hare-haren Iran kan jiragen ruwan Birtaniya REUTERS/Matt Spetalnick
Talla

Mahukunta a Bahrain, karamar kasa da ke dauke da babban sansanin jiragen yakin Amurka mai lamba ta biyar, sun ce ana gudanar da taron ne domin tattaunawa game da matsalar tsaro da kuma kyautata dangantaka a tsakanin kasashen yankin.

Sanarwar da mahalarta taron suka fitar ta yi kakkausar suka ga kasar Iran, sakamakon abin da suka kira hare-hare da kuma mara wa ayyukan ta’addanci da kasar ke yi.

Amurka ma ta bi sahun kasashen na yankin Gulf wajen zargin Iran da hannu a hare-haren da ake cewa an kai wa jiragen dakon mai na wasu kasashen Larabawa cikin ‘yan makonnin da suka gabata, zargin da Iran ta musanta.

An kara shiga zaman tankiya a yankin tekun Fasha ne bayan da Iran ta kame wani jirgin dakon mai na kasar Birtaniya a ranar 19 ga watan Yuli, jirgin da Iran ke zargin cewa ya karya doka tare da kin mutunta sakon gargadin da aka aike wa matukansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.