Dubun-dubatar mutane ne dai, suka rufe fuskokinsu tare da yin dandazon da nufin sake rufarwa Ofishin China da ke arewacin yankin Yuen Long kamar yadda suka yi a makon jiya.
Mako na 7 kenan Hong Kong na fuskantar kazamar zanga-zangar boren ga gwamnati tun bayan kudirin da ya nemi fara aikewa da masu laifi China don fuskantar hukunci, mayakin da ya ci karo da kundin tsarin mulkin da ma yarjejeniyar mika yanking a China da aka cimma da Birtaniya.
Duk da cewa gwamnati ta janye kudirin dokar, yanu haka masu zanga-zangar na neman murabus din shugabar yankin tare da bin kadion hakkokin wadanda jami’an tsaro suka ciwa zarafi yayin zanga-zangar.