Ma’aikatar tsaron Koriya ta Kudu ta ce daya daga cikin makaman ba’a taba ganin irin sa ba, yayin da ya yi tafiyar kilomita 690 kafin ya fada a teku.
Wannan shi ne karo na farko da Koriyar ke gwajin makamai tun bayan ganawar da aka yi tsakanin shugaba Donald Trump da Kim Jong Un a watan jiya, wanda bai samu nasara ba.
Masu sa ido na bayyana cewar atisayen sojin da akeyi tsakanin Amurka da Koriya ta kudu na daga cikin abinda ya harzuka Koriya ta Arewa wajen gudanar gwajin makaman.