Isa ga babban shafi
Hong Kong

Masu bore a Hong Kong na neman a soke dokar da ta haifar da rikici

A Hong Kong masu Shirya zanga zangar adawa da gwamnatin Hong Kong sun ce babu abinda ya sauya dangane da matsayin jagorar gwamnatin kasar Carrie Lam na cewar dokar da ake shirin yi wadda ta haifar da zanga zanga ta mutu.

Carrie Lam Shugabar Gwamnatin Hong Kong
Carrie Lam Shugabar Gwamnatin Hong Kong REUTERS/Tyrone Siu
Talla

Masu zanga zangar sun ce muddin Lam taki biya musu bukatun da suka gabatar guda 5, toh zasu cigaba da zanga zangar da suke.

A jawabin da tayi yau, Lam ta bayyana cewar dokar da ake takaddama akan ta mutu, Shugabar Gwamnatin Hong Kong ta ci gaba da cewa:

Har yanzu akwai shakkun dake cigaba da tafiya akan sahihancin gwamnati ko kuma damuwar cewar ko gwamnati zata sake fasalin yin wata doka a majalisar dokoki, saboda haka uwargida Lam ta jadadda cewa, babu wani shiri, dokar ta mutu.

Ana dakon wata sabuwar zanga-zanga a Hong Kong cikin yan lokuta masu zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.