Tanaji Kamble, mai Magana da yawun hukumar agajin gaggawa a Mumbai, ya ce baya ga wadanda suka mutu, wasu da dama sun jikkata sakamakon faduwar katangar a unguwar marasa galihu.
Hukumomin birnin sun bayyana yau Talata a matsayin ranar hutu, inda suka bukaci mutane su zauna a gidajen su domin kaucewa ambaliyar da aka samu wadda ta tilasta rufe makarantu da kuma soke tashin jirage sama da 100.