Wong mai shekaru 22 da aka sallama daga gidan yari a ranar Litinin, na cikin wadanda suka jagoranci wata gagarumar zanga-zangar tabbatar da tsarin dimokradiya a shekarar 2014 a Hong Kong.
A yayin zantawa da manema labarai jim kadan da sakin sa daga gidan kaso, Wong ya ce, yana bukatar gajeren lokaci domin gudanar da wani nazari, amma a cewarsa, tabbas zai shiga a dama da shi a sabuwar zanga-zangar adawa da kudirin dokar tasa keyar masu laifi zuwa China domin fuskantar hukunci.
An garkame matashin dalibin ne a gidan yari bayan an same shi da laifin yi wa doka karan tsaye a lokacin zanga-zangar 2014 wadda ta bukaci gudanar da zabuka cikin tsarin dimokradiya.
A ranar Lahadin da ta gabata, kimanin al’ummar Hong Kong miliyan 2 ne suka fantsama kan tituna domin ci gaba da zanga-zangar adawa da kudirin dokar tasa keyar masu laifin, kodayake jami’an ‘yan sanda sun ce, adadin masu boren bai wuce dubu 338 ba.