Isa ga babban shafi
Asiya

Zanga zangar adawa a Hong Kong

Dubban Mutane ne yau Laraba suka sake gudanar da zanga zangar adawa da shirin amincewa da wata doka da zata bada damar tisa keyar wanda ake zargi da aikata laifi daga Hong Kong zuwa China domin yi masa shari’a.

Masu zanga-zanga a Hong-Kong
Masu zanga-zanga a Hong-Kong REUTERS/Thomas Peter
Talla

Masu zanga zangar akasarin su matasa da dalibai sun yiwa ofisoshin gwamnati kawanya, inda suka hana motoci motsawa domin ganin Majalisa tayi watsi da dokar.

Ganin yadda tururuwar masu zanga zangar ta mamaye jami’an tsaron da suke cikin damarar ko ta kwana, shugabannin Majalisa sun bayyana dakatar da mahawara kan dokar zuwa wani lokaci nan gaba.

A shekara ta 2017 aka zabi Carrie Lam a matsayin sabuwar shugaba Hong Kong bayan kwamitin da ke goyon bayan China sun kada kuri’ar.

Zaben dai a lokacin ya fuskanci suka daga ‘yan kasar da suke son a ba kowa yancin kada kuri’a, maimakon wasu tsiraru.

Tun kafin kada kuri’a kamar dai yada masu sharhi suka yi la’akari aka yi hasashen Carrie Lam mataimakiya ga shugaban Hong Kong da China ke ra’ayi za a zaba.

Kwamitin zaben ya kunshi mambobi 1,194, kuma Lam ta lashe zaben ne da yawan kuri’u 777.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.