Isa ga babban shafi
Duniya

Bong Joon-Ho ya lashe Palme D’or na Cannes

An kamala bikin nuna fina-finai na Cannes a kasar Faransa karo na 72 a duniya, bikin dai ya samu halartar mayan masu tsara fina-finai na Duniya dama Gwamnatocin kasashe.Taron dai ya samu hallatar fitattun masu tsara fina-fanai daga sassa dabam-dabam na Duniya.

Bong Joon-Ho ya lashe  Palme D’or na  Fina-Finai a Cannes dake kasar Faransa
Bong Joon-Ho ya lashe Palme D’or na Fina-Finai a Cannes dake kasar Faransa Reuters
Talla

A wannan karon dai ‘yan yankin Turai ne suka samu nasara lashe kyaututuka da dama, Mati Diop yar Faransa da kuma Senegal ce ta lashe kyautar fim din daya fi ko wane tasiri a Duniya.

Bong Joon-Ho dan Koriya ta Kudu na daya daga cikin mutane da suka samu kyauta da ta fi kowace a wanan taron da ake kira Palme D’or.

Bong dai ya bayana matukar farin cikin sa tare da nuna yabawa ga daukaci wadanda suka taimaka masa wajen samun wannan nasara.

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ta bakin mai magana da yahun sa ya bayyana goyan bayan sa, ga duk wani tsari da masu tsara fina finai ke bukata a kasar, domin samar da cigaba a harkokin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.