Isa ga babban shafi

Saudiya ta kira taron gaggawa kan barazanar Iran a yankin Gulf

Kasar Saudi Arabia ta kira taron gaggawa da takwarorinta kasashen yankin Gulf dai dai lokacin da ake ci gaba da samun baraka tsakaninta da Iran, Inda Saudiyan ke cewa ba ta fatan yaki da Iran amma a shirye ta ke wajen kare kanta daga barazanar Iran a yankin.

Sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud
Sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud reuters
Talla

Kiran taron gaggawan na Saudiya na zuwane kwanaki kadan bayan hare-haren da ‘yan tawayen Houthi suka kaddamar kan bututun man ta da tankokinta wanda kasar ke cewa harin ya faru ne bisa umarnin Iran.

Sarki Salman ya kira taron gaggawan ne har guda biyu ciki har da wanda zai gudana a Mecca ranar 30 ga watan nan, dai dai lokacin da Amurka ta ajje wasu tarin jiragenta na yaki don bayar da tsaro ga kasashen yankin, baya ga yunkurin girke dakarun sojinta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.