Isa ga babban shafi
India-Zabe

An kammala zagaye na 7 na zaben India

Yau lahadi aka kammala zagaye na 7 kuma na karshe a zaben India da aka shafe fiye da wata guda ana gudanarwa, zaben da zai fayyace makomar Firaminista Narendra Modi wanda ke fatan ci gaba da kasancewa a karagar mulki a wa’adi na biyu.

Wasu masu kada kuri'a a zaben kasar India da aka kammala zagaye na 7 kuma na karshe a yau lahadi
Wasu masu kada kuri'a a zaben kasar India da aka kammala zagaye na 7 kuma na karshe a yau lahadi REUTERS/Adnan Abidi
Talla

Hukumar zaben kasar ta sanar da cewa an kulle rumfunan zabe da misalin karfe 12 da rabi na ranar yau, inda ta ce za ta fara kirgen kuri’un na kimanin mutane miliyan 900 da suka kada kuri’a a zaben kasar nan da ranar Alhamis mai zuwa.

Zaben na India wanda shi ne mafi yawan jama’a da ke kada kuri’a haka zalika mafi daukar tsawon lokaci ana yi a duniya, akwai hasashen a wannan karon jam’iyyar Firaminista Modi ta BJP ka iya rasa rinjayenta a Majalisar kasar.

A shekarar 2014 dai jam’iyyar ta Modi ta yi gagarumar nasarar lashe kujeru 282 cikin 543 da kasar ke da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.