Isa ga babban shafi
India-Zabe

Indiyawa miliyan 100 na kada kuri'a a zagayen karshe na zaben kasar

Al’ummar India fiye da mutum miliyan 100 ne yanzu haka ke ci gaba da kada kuri’a a birnin Delhi da sauran sasan kasar yayin zagayen karshe na zaben kasar dai dai lokacin da bangarorin adawa suka hade waje guda don ganin sun hana Firaminista Narendra Modi damar zuwa wa’adi na biyu na mulkin kasar.

Wasu mata kenan a rumfunan zabe yayin kada kuri'a a babban zaben kasar India
Wasu mata kenan a rumfunan zabe yayin kada kuri'a a babban zaben kasar India REUTERS/Adnan Abidi
Talla

Zaben wanda za a shafe kwanaki 39 a na yi a sassan kasar, wannan ne zagaye na bakwai kuma na karshe tun faro shi a ranar 11 ga watan Aprilu inda ake saran kammala shi a ranar 19 ga watan nan.

Sai dai da alama hadewar jam’iyyun adawar zai haddasa babban kalubale ga Firaminista Modi na Jam’iyyar BJP wanda ake ganin abu ne mai wuya idan bai nemi goyon baya don kafa gwamnatin hadaka ba.

A ranar 23 ga watan nan ne za a fara kirga kuri’u tare da sanar da wanda ya yi nasara a zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.