Isa ga babban shafi
Japan

Sarki Akihito na Japan ya yi murabus

Sarkin kasar Japan Akihito mai shekaru 85 a duniya ya sauka daga karagar mulki a yau Talata, karo na farko da aka taba samun faruwar hakan a kasar cikin fiye da shekaru 200.

Sarki Akihito na Japan
Sarki Akihito na Japan 路透社。
Talla

Da safiyar yau ne Sarki Akihito ya mika duk wasu kayakin tafiyar da sarautar kasar da ke hannunsa ga fadar da ke birnin Tokyo, kayakin da suka hada da sandar mulki takubba da kuma wata sarkar gado.

Bayan murabus din sarkin mai shekaru 85 da ake alakantawa da yawan shekaru, a gobe Laraba ne kuma za a nada dansa Naruhito mai shekaru 59 don ci gaba da jan ragamar mulkin.

A jawabansa na bankwana bayan sanya hannu kan takaddun ajje aiki, Sarki Akihito ya yi fatan alkhairi tare da fatan wanzuwar zaman lafiya da salama ga kasar ta Japan da ma duniya baki daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.