Saurare Saukewa Podcast
 • 06h00 - 06h17 GMT
  Labarai 24/01 06h00 GMT
 • Labarai 06h00 - 06h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 25/01 06h00 GMT
 • Shirye-shirye 06h06 - 06h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 25/01 06h06 GMT
 • 06h17 - 06h27 GMT
  Shirye-shirye 24/01 06h17 GMT
 • 07h00 - 07h17 GMT
  Labarai 24/01 07h00 GMT
 • Labarai 07h00 - 07h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 25/01 07h00 GMT
 • Shirye-shirye 07h06 - 07h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 25/01 07h06 GMT
 • 07h17 - 07h27 GMT
  Shirye-shirye 24/01 07h17 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h30 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 24/01 16h00 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 25/01 16h00 GMT
 • Shirye-shirye 16h06 - 16h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 25/01 16h06 GMT
 • Labaran Duniya 16h30 - 16h40 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 24/01 16h30 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 25/01 16h30 GMT
 • Shirye-shirye 16h36 - 16h56 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 25/01 16h36 GMT
 • Ra'ayoyin Masu Saurare 16h40 - 16h55 GMT Litinin-Jumma`a
  Jin Ra'ayoyin Masu Saurare 24/01 16h40 GMT
 • Labarai 20h00 - 20h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 19/01 20h00 GMT
 • 20h00 - 20h17 GMT
  Labarai 24/01 20h00 GMT
 • Shirye-shirye 20h06 - 20h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 19/01 20h06 GMT
 • 20h17 - 20h27 GMT
  Shirye-shirye 24/01 20h17 GMT
Domin more wa abubuwan da ke ciki, dole ne a tabbatar da cewa an sanya Flash Domin shiga sai an hada cookies a cikin shafin bincike
Asiya

India ta yi makokin cika shekaru 100 da kisan kiyashin Amristar

media Mataimakin shugaban kasar India Venkaiah Naidu a wajen taron makokin cika shekaru 100 da kisan kiyashin turawan mulkin mallaka a Amritsar AFP/NARINDER NANU

Kasar India ta yi makokin cika shekaru 100 da kisan kiyashin da sojojin mulkin mallaka na Birtaniya suka yiwa al’ummar Amristar, kisan kiyashi mafi muni da tarihin India ba zai manta ba.

Kisan kiyashin da Indiyawa kewa lakabi da Jallianwala Bagh, kasar na ikirarin sojojin mulkin mallakar sun bude wuta kan fararen hula masu neman ‘yanci galibi mata da kananan yara inda suka kashe fiye da mutum dubu ko da dai Birtaniyar na cewa mutane 379 kacal aka kashe.

Cikin sakon da Firaminisatan India Narendra Modi ya gabatar ga al'ummar ta Armristar ya ce ranar babbar abin bakin ciki ne ga al'ummar kasar.

Modi wanda ya samu wakilcin mataimakin shugaban kasar, Venkaiah Naidu a wajen taron makokin cika shekaru darin ya ce makamantan cin zarafin da indiyawa suka fuskanta daga sojojin mulkin mallaka ne ke tilastasu gudanar da ayyukan da dole su kasance ababen sha'awa.

A ranar 13 ga watan Aprilun 1919 ne dai kisan kiyashin ya faru, wanda shekaru 100 kawo yanzu Birtaniya ta gaza ba da hakuri ko sanar da dalilin afkuwarsa.

Cikin jawaban jajantawa da Firaminista Theresa May ta gabatar a zaman majalisar kasar, ta nuna rashin jin dadinta da abin da ya faru shekaru 100 da suka gabata, ko da dai ta gaza aikewa da sakon neman yafiya.

Ko a shekarar 2013 lokacin da Firaministan Birtaniya na wancan lokaci David Cameron ya kai ziyarar jaje a irin wannan rana kasar ta Indiya ya bayyana lamarin da abin kunya amma ya gaza bayar da hakuri.

A game da wannan maudu'i
Sharhi
 
Yi hakuri lokacin ci gaba da kasancewa da mu ya kure