Yakin Yemen ya haifar da tagayyarar mutane mafi muni - MDD
Majalisar Dinkin Duniya, ta ce Yakin Yemen ya haifar da tagayyarar fararen hula mafi muni a duniya da aka gani a baya bayan nan.
Wallafawa ranar:
Rahoton Majalisar yace Yakin tsakanin ‘yan tawayen Houthi da dakarun wasu kasashen Larabawa a karkashin jagorancin Saudiya, ya hallaka sama da fararen hula dubu 10, yayinda wasu sama da dubu 60 suka jikkata, sai kuma akalla 'yan kasar miliyan 3 da dubu 300 da suka rasa muhallansu.
Rahoton ya kara da cewa akalla yara yan kasa da shekaru 5, miliyan da 1 dubu 800 ke fama da yunwa a kasar, bayaga wasu dubu 85 da yunwar ta hallaka a tsakanin Afrilu na 2015 zuwa Oktoban 2018.
Zalika a bangaren ilimi, sama da makarantu dubu 2 da 500 ne basa aiki, biyu bisa ukunsu kuma yakin kasar ta Yemen ne ya ragargaza su, hakan tasa kimanin kananan yara miliyan 7 ne basa zuwa makaranta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu