Isa ga babban shafi
Amurka-Saudiya

Amurka na daf da janye dakarun ta daga fagen yakin Yemen

Majalisar dattijan Amurka ta kada kuri’ar amincewa da janye dakarun kasar daga yakin Yemen, dakarun da ke taimakawa mayaka Larabawa da Saudiya ke Jagoranta, wadanda kungiyoyin kare hakkin dan adam ke zargi da hallaka fararen hula, hadi da azabtar da yunwa.

Zaman tattaunawa don kawo karshen yakin Yemen a Amman na kasar Jordan.
Zaman tattaunawa don kawo karshen yakin Yemen a Amman na kasar Jordan. REUTERS/Muhammad Hamed
Talla

‘Yan majalisar dattijan na Amurka 54 ne suka goyi bayan kudurin yayinda 46 suka jefa kuri’ar kin amincewa.

Kungiyoyin agaji sun kiyasta cewa fararen hula akalla dubu 60 suka hallaka a Yemen, wasu kananan yara dubu 85 kuma sun hallaka a dalilin bala’in yunwa, tun bayan soma yakin kasar a shekarar 2014.

A cikin watan Fabrairu ne majalisar wakilan Amurka karkashin rinjayen Jam’iyar Democrat, ta amince da wani kudirin doka da zai kawo karshen goyon bayan da Amurkar ke bai wa Saudiya a yakin da take jagoranta a Yemen.

Da dama daga cikin mambobin Majalisar sun kuma bukaci shugaba Donald Trump da ya tsaurara tsare-tsarensa kan Saudiya.

A karon farko kenan da Majalisar ta goyi bayan kudirin dokar yaki a Yemen, in da mambobinta 248 suka kada kuri’ar amincewa da kudirin, yayin da 177 suka nuna rashin amincewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.