Isa ga babban shafi
Taliban-Afghanistan

Taliban ta yi watsi da tayin tattaunawar sulhu da Afghanistan

Kungiyar Taliban ta yi watsi da tayin tattaunawa da gwamnatin shugaba Ashraf Ghani na Afghanistan, yayin da wakilan ta ke cigaba da tattaunawar zaman lafiya da wakilan gwamnatin Amurka.

Wasu kwamandojin kungiyar Taliban
Wasu kwamandojin kungiyar Taliban sputnik
Talla

Rahotanni sun ce wakilan kungiyar na cigaba da gudanar da tarurruka a Doha da kuma Moscow, inda su ke ganawa da wakilan kasashen duniya daban daban, yayin da suka sa kafa suka shure duk wata bukatar ganawa da gwamnatin Afghansitan.

Masana sun ce Rasha da Iran na kokarin janyo hankalin Taliban domin kulla dangantaka mai karfi, saboda matsayin su na ganin Amurka ta janye daukacin dakarun ta a cikin kasar su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.