Isa ga babban shafi
India

Mabiya addinin Hindu sun wanke zunubansu a kogi

Miliyoyin mabiya addinin Hindu sun yi wanka a wani kogi mai tsarki domin wanke zunubansu, in da aka rika ba su tokar gawarwakin shehunansu domin shafawa a jiki da kuma gudanar da ibada.

Wasu daga cikin mahalarta bikin wanke zunubai a kogunan India masu tsarki
Wasu daga cikin mahalarta bikin wanke zunubai a kogunan India masu tsarki ©REUTERS/Danish Siddiqui
Talla

Shi dai wannan biki da ake yi wa lakabi da Kumbh Mela, na bai wa mabiya addinin Hindu damar tashi da asuba a garin Allahabad domin wanka a kogunan Ganges da Yamuna da kuma Saraswathi wadanda suke kallon su a matsayin masu tsarki.

Mabiya addini sun yi imanin cewar, wanka a cikin wadanan koguna na wanke daukacin zunuban da suka yi, kuma suna kallon ranar 4 ga watan Fabarairu a matsayin rana mai tsarki na fara bikin da za a kwashe wata guda ana gudanar da shi har zuwa ranar 4 ga watan Maris mai zuwa.

'Yan Sanda 30,000 aka jibge domin samar da tsaro, yayin da gwamnati ta kashe Dala miliyan 40 domin tsaftace ruwan, kana kuma an samar da ban-daki 40,000 ga masu halartar bikin.

Akalla mabiya addinin Hindu miliyan 12 suka halarci sharen fagen bikin da akayi a watan Janairu, yayin da ake saran mabiya miliyan 120 su halarci bikin gadan-gadan da aka fara a yau Litinin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.