Isa ga babban shafi
Iran

Iran ta yi nasarar gwajin sabon makami mai linzami

Iran ta sanar da samun nasarar gwajin makami mai linzamin da ta kera da ke iya tafiyar sama da nisan kilomita dubu 1 da 350.

Wasu daga cikin sabbin makamai masu linzami a birnin Teheran, wadanda da Iran ta yi nasarar gwajinsu. 2/2/2019.
Wasu daga cikin sabbin makamai masu linzami a birnin Teheran, wadanda da Iran ta yi nasarar gwajinsu. 2/2/2019. AFP
Talla

Gwajin sabon makamakin na Iran ya zo a daidai lokacin da kasar ke ci gaba da bukukuwan cika shekaru 40, da kafuwar Jamhuriyar Musulunci, bayan juyin juya halin shekarar 1979.

Ministan tsaron Iran Amir Hatami, ya ce an gudanar da gwajin makamin mai linzami daga tazarar kilomita dubu 1 da 200, kuma yayi nasarar kaiwa inda aka saita shi.

A shekarar 2015 Iran ta cimma yarjejeniyar dakatar da shirinta na inganta makamashin nukilya tsakaninta da manyan kasashen duniya, sai dai ta ci gaba da kera manyan makamai masu linzami, daya daga cikin matakan da yasa Amurka ficewa daga yarjejeniyar ta 2015 a watan Mayu na shekarar bara, tare da kakaba mata takunkuman karya tattalin arziki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.