Isa ga babban shafi
China-Korea

Kim Jong Un na ziyara a China gabanin sake ganawa da Trump

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un ya isa birnin Beijing na China don ganawa da shugaban kasar Xi Jinping game da shirye-shiryen ganawarsa ta biyu da Donald Trump na Amurka.

Wannan dai ne karo na 4 da Kim ke ziyartar China tun bayan daukar matakin ajje shirinsa na mallakar makaman nukiliya.
Wannan dai ne karo na 4 da Kim ke ziyartar China tun bayan daukar matakin ajje shirinsa na mallakar makaman nukiliya. ©KCNA via REUTERS
Talla

Ziyarar wadda ke zuwa a bazata, ba tare da sanin kafofin labarai ba, ana ganin ba ta rasa nasaba da bukatar Trump ta neman sake ganawa da Kim la’akari da yadda China ke matsayin babbar abokiyar Korea ta arewan haka zalika kasa daya tilo da ke bata dauki duk da matsin lambar da ta ke fuskanta daga kasashen duniya sakamakon takunkuman Amurka.

Ma’aikatar harkokin wajen China ta tabbatar da cewa Shugaba Xi zai gana da Kim don tattaunawa kan batutuwa da dama, ko da dai kai tsaye ma’aikatar ba ta bayar da haske kan batun da shugabannin za su tattauna ba.

Kim Jong Un bisa rakiyar matarsa Ri Sol Ju da wasu manyan jami’an gwamnatinsa sun yi amfani da wani karamin jirgin kasa ne daga Koriyar zuwa China bisa gayyatar shugaba Xi a cewar ma’aikatar yada labaran kasar.

Ziyarar wadda it ace karo ta 4 a baya-bayan nan da Kim ya kai China na zuwa ne mako guda bayan barazanar da ya yi ta janyewa daga duk wata tattaunawar sulhu da Amurka, matukar ta ci gaba da yi masa matsin lamba game da takunkuman da ta kakaba masa.

Masana alakar kasashe dai na ganin kulluwar alakar Kim da Xi baya rasa nasaba da kokarin da Kim ke yin a ganin China ta taimaka don ya samun raguwar matsin lambar da yak e fuskanta daga kasashen duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.